Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin janye ƙwararrun jami’an Diflomasiyyar ƙasar daga ƙasashen duniya 29
Wannan mataki na cikin yunƙurin sake fasalin tsarin diflomasiyyar Washington domin ya dace da manufar shugaban ƙasar mai take “America First”.
Bayanai sun bayyana cewa matakin janye jakadun ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ƴan majalisar dokokin ƙasar, yayin da ƙungiyar wakilan jami’an diplomasiyyar Amurka ke ƙorafi kan wannan mataki.
Wasu jami’an Ma’aikatar harkokin wajen Amurka biyu, sun shaidawa kamfanin dillancin labaran AP cewa, an sanar da shugabannin ofisoshin jakadanci na aƙalla kasashe 29 a makon da ya gabata cewa wa’adin aikinsu zai ƙare a watan Janairu mai kamawa.
Nahiyar Afirka ce ta fi fuskantar wannan mataki, inda aka dawo da jakadu daga kasashe 15.
Ƙasashen sun haɗa da Najeriya, Burundi, Cameroon, Cape Verde, Gabon, Cote d’Ivoire, Madagascar, Mauritius, Niger, Rwanda, Senegal, Somalia, Algeria, Egypt da Uganda.
Dukkanin jami’an diflomasiyyar da abin ya shafa sun fara aiki a matsayin wakilan Amurka a ƙasashen ne tun zamanin Joe Biden.
Rahotanni sun ce wannan mataki ba yana nufin cewa jakadun zasu rasa aikinsu bane, a’a zasu koma Washingon ne don karɓar wasu ayyukan na daban.
Har kawo ya zuwa yanzu Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba ta yi tsokaci kan adadin jakadun da aka dawo da su ba, amma ta kare matakin, tana mai bayyana shi a matsayin “tsari na al’ada a kowace gwamnati”.