Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTikTok ta dakatar da yin bidiyo kai tsaye da daddare saboda yawaitar...

TikTok ta dakatar da yin bidiyo kai tsaye da daddare saboda yawaitar batsa.

TikTok ta dakatar da damar yin bidiyo kai tsaye da daddare a Najeriya bayan karuwar bidiyo masu ɗauke da batsa,tare da ci gaba da gudanar da binciken tsaro a shafin.

Kamfanin ya sanar da takunkumi ga masu amfani da TikTok a Najeriya a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa yana gudanar da nazarin tsaro domin “tabbatar da cewa shafin zai ci gaba da aiki domin a rika amfani da shi cikin mutunci.

TikTok bai bayyana tsawon lokacin da wannan dakatarwar za ta ɗauka ba.

Bayanan cikin gida da aka bayyana a taron tsaron TikTok na Yammacin Afrika da aka gudanar a Dakar, Senegal, sun nuna cewa ana ta ƙara amfani da yin bidiyo kai tsaye wajen aikata laifuffukan da suka saba ka’ida a Najeriya.

Kamfanin ya bayyana cewa a wata na biyu na 2025 kaɗai, ya yi gargaɗi kuma ya cire damar samun kuɗi daga sama da bidiyo da aka yi kai tsaye miliyan 2.3, tare da hukunta fiye da masu shafuka miliyan daya saboda karya dokokin samun kuɗi.

Najeriya ta bayar da rahoton bidiyo kai tsaye 49,512 da aka dakatar a wannan watan.

A ‘yan watannin nan, bidiyo kai tsaye na TikTok da ake kai tsaye da daddare a Najeriya sun ƙara yin suna da bidiyon batsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments