Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƘungiyar NATO na gudanar da taro game da rikicin Rasha da Ukraine.

Ƙungiyar NATO na gudanar da taro game da rikicin Rasha da Ukraine.

NTO tana gudanar da taro kan matsalolin tsaro tsakanin Rasha da Ukraine

Ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar Nato na taro domin tattauna batun yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine da kuma batutuwan da suka shafi tsaro.

A yayin jawabin buɗe taro, shugaban ƙungiyar, Mark Rutte ya ce Rasha na shirin yin fito na fito da su, sannan Rasha ta karya dokokin ƴancin sararin samaniyyar ƙasashe.

Ya ƙara da cewa Russia tana aiki da China da North Korea da Iran domin lalata ƙasashensu da kuma raba kan ƙasashe dangane da dokokin ƙasa da ƙasa,in ji Rutte.

Daga ƙarshe mista Rutte ya ce dole ne ƙasashen ƙungiyar su haɗa ƙarfi wuri guda su kuma nuna shi.

SourceBBC hausa
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments