Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya ce an lalata aƙalla turakun wutar lantarki 10 a yankin Kano cikin watanni biyar.
Manajan TCN na yankin Kano, Injiniya MK Bello, ne ya bayyana hakan yayin gangamin wayar da kan jama’a a garin Paki, Ƙaramar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna.
Ya ce turakun suna kan hanyoyin wutar lantarki na Kano zuwa Zariya, Kano zuwa Katsina da Kano zuwa Hadejia. Ya ƙara da cewa an kama mutane sama da 33 da ake zargi da lalata kayayyakin kamfanin.
Mataimakin Babban Manajan TCN, Injiniya Ibrahim Aliyu, ya ce an lalata turaku sama da 20 a Kunkumi kaɗai. Ya buƙaci jami’an tsaro su gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu.
Aliyu ya kuma gargaɗi jama’a kan gina gidaje kusa da layukan wutar lantarki, yana mai cewa dole ne a bar tazarar mita 15 zuwa 25. Shi ma Hakimin Paki, Alhaji Ja’afaru Aliyu Paki, ya yi alƙawarin taimakawa wajen kare kayayyakin more rayuwa.