Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiSadio Mane ya bayyana kalaman da Cristiano Ronaldo ya yi masa bayan...

Sadio Mane ya bayyana kalaman da Cristiano Ronaldo ya yi masa bayan wasan Al Nassr

Ɗan wasan ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya, Sadio Mane, ya bayyana wasu kalamai da ya ce kyaftin ɗin ƙungiyar, Cristiano Ronaldo, ya faɗa masa bayan kammala wasan da suka buga da Al Kholood ranar Alhamis.

Mane ya ce Ronaldo ya zo wurinsa bayan wasan, inda ya furta kalaman da suka taɓa zuciyarsa sosai.

A cewarsa, Ronaldo ya ce yana ƙaunarsa a matsayin ɗan’uwa, tare da nuna godiya gare shi saboda taimakonsa wajen matsowa kusa da burinsa na zura ƙwallaye 1,000 a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

Ya ƙara da cewa Ronaldo ya bayyana masa cewa yanzu ba ya kallonsa a matsayin abokin wasa ko aboki kawai, a’a, yana ɗaukarsa a matsayin ƙaninsa.

Mane ya ce kalaman sun matuƙar faranta masa rai, domin yana da matuƙar girmamawa ga Ronaldo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments