Lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima Fagge, ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta nemi afuwar Isa Ali Pantami da Abdulsalam Gwarzo, tare da biyansu diyya kan cire sunayensu daga cikin ’yan takarar zaɓen 2027.
Abba Hikima ya bayyana cewa tun farko bai kamata hukumar ta cire Pantami da Gwarzo daga takarar gwamna a jihohinsu ba.
Ya ce matakin da INEC ta ɗauka na cire su daga cikin ’yan takara ya kamata ya sa hukumar ta ɗauki alhakin abin da ya faru, ta hanyar ba su haƙuri da kuma biyan su diyya.
Sai dai wannan kira na Abba Hikima Fagge na zuwa ne bayan INEC ta sanar da mayar da Pantami da Gwarzo cikin jerin ’yan takarar zaɓen 2027, yayin da ake ci gaba da shari’o’in da suka shafi takararsu a gaban kotuna.