Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya, domin gudanar da ibadar Umara da kuma yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Jaridar ta ruwaito cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana cewa yayin zamansa a Makka, Tinubu zai gudanar da ibadar Umara tare da roƙon Allah Ya ba Najeriya da al’ummarta zaman lafiya, shiriya da albarka.
Kafin tafiyarsa, shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu kayayyakin aiki da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta saya domin inganta ayyukanta.
Za a gudanar da ƙaddamarwar ne a wani ɓangare na musamman na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya a mako mai zuwa bayan kammala ibadar Umara.