Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yi Allah-wadai da kisan Sheikh Masussuka

Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan Sheikh Masussuka

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da almajirinsa, Adamu Abubakar, a Dutsin-Ma, Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga ne suka kashe mutanen biyu a wani hari da suka kai musu a cikin mota a yammacin ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, Tinubu ya bayyana alhininsa kan kisan, yana mai cewa irin wannan aika-aika ta saɓa wa ƙimar zaman lafiya da kuma mutunta rayuwar ɗan’adam.

Shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, mabiyansu, gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar bisa wannan babban rashi.

Haka kuma, Tinubu ya umarci rundunar ’yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su ƙarfafa binciken da ’yan sandan Jihar Katsina suka fara, domin gano waɗanda suka aikata kisan, cafke su da kuma gurfanar da su a gaban shari’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments