Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiSheikh Gumi ya bukaci a kwantar da hankali bayan kashe Sheikh Masussuka

Sheikh Gumi ya bukaci a kwantar da hankali bayan kashe Sheikh Masussuka

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da barin hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin da ya dace bayan kashe Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a jihar Katsina.

Sheikh Gumi ya bayyana kisan a matsayin babban kuskure da ka iya haddasa rikici tsakanin Musulmi, yana gargadin cewa akwai yiwuwar wasu su yi amfani da lamarin wajen haifar da rudani da rarrabuwar kawuna.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bukaci jama’a da kada su dauki doka a hannunsu, yana mai jaddada muhimmancin mika batutuwan tsaro ga hukumomin da suka dace.

Ya kuma yi nuni da ayoyin Alkur’ani, ciki har da Suratun Nisa’i 4:83 da Suratun Nur 24:63, domin karfafa kira ga jama’a da su guji yada bayanan da ba a tantance ba da kuma duk wani mataki da zai iya haddasa fitina.

A karshe, Sheikh Gumi ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya, Ya kuma kawar da rikici da rarrabuwar kawuna a cikin al’ummar Musulmi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments