Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiShettima ya soki Atiku kan kwarewar jagorantar tattalin arzikin Najeriya

Shettima ya soki Atiku kan kwarewar jagorantar tattalin arzikin Najeriya

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ba shi da ƙwarewar da ake buƙata wajen tafiyar da tattalin arzikin zamani.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin taron koli na tattalin arzikin Najeriya karo na 32 da ake gudanarwa a Abuja.

A yayin taron, Shettima ya soki shawarar Atiku ta dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa matakin zai iya mayar da ƙasar baya domin biyan buƙatun siyasa.

Haka kuma, Shettima ya yi tsokaci kan karatun Atiku a fannin tsafta a Makarantar Kiwon Lafiyar Muhalli ta Kano, yana mai cewa hakan ba ya nuna ƙwarewar tafiyar da tattalin arzikin zamani.

Sai dai Shettima ya kare matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa la’akari da halin da tattalin arzikin ƙasar yake ciki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments