Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiRauni zai hana Chukwueze taimaka wa Super Eagles a wasannin share fage...

Rauni zai hana Chukwueze taimaka wa Super Eagles a wasannin share fage na AFCON

Ana sa ran Samuel Chukwueze zai rasa wasannin neman gurbin shiga AFCON 2027 da Super Eagles za ta buga da Tanzania saboda raunin ƙugu da yake jinya.

Chukwueze ya ji raunin ne a wasan da AC Milan ta doke Atalanta da ci 3-2, inda aka cire shi daga wasa. Duk da cewa an yi hasashen zai murmure cikin makonni biyu, rahotanni sun nuna cewa zai ɗauki ƙarin lokaci.

Rashin ɗan wasan na iya shafar Super Eagles, wadda za ta karɓi baƙuncin Tanzania a Uyo ranar 13 ga Nuwamba, kafin ta ziyarce ta a Dar es Salaam.

Najeriya tana matsayi na biyu a rukunin L da maki uku, yayin da Guinea-Bissau ke kan gaba da tazarar maki uku bayan ta doke Super Eagles da ci 3-0.

Najeriya na buƙatar samun sakamako mai kyau a sauran wasannin domin kauce wa rasa gurbin AFCON 2027, abin da bai faru da ita ba tun gasar shekarar 2017.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments