Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiAkwai alaka mai karfi tsakanin Tinubu da Arewa – Uba Sani

Akwai alaka mai karfi tsakanin Tinubu da Arewa – Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce alakar da ke tsakanin al’ummar Arewa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu tana da ƙarfi, yana mai tabbatar masa cewa yankin na tare da shi.

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce alakar da ke tsakanin al’ummar Arewa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu tana da ƙarfi, yana mai tabbatar masa cewa yankin na tare da shi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ranar Asabar, bayan ƙaddamar da kamfen ɗin neman sake zaɓen Tinubu na 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC a Kaduna.

Uba Sani ya ce dimbin mutanen da suka fito domin tarbar Tinubu daga filin jirgin sama zuwa filin taro sun nuna irin goyon baya da amincewar da suke da shi ga shugabancinsa.

Ya kuma yaba wa Tinubu kan ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a Kaduna da sauran jihohin Arewa maso Yamma, musamman a fannonin ilimi, lafiya, noma, sufuri da samar da ababen more rayuwa.

Gwamnan ya ce al’ummar Arewa za su haɗa kai wajen neman nasarar Tinubu a zaɓen Janairun 2027, yana mai cewa za su yi aiki tare domin tabbatar da sake zaɓensa da kuma ci gaban Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments