Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke ’yar TikTok, Amani Ishaq, tare da wasu mata biyu bisa zargin yaɗa bidiyoyin da ake ganin sun saɓa wa tarbiyya a kafafen sada zumunta.
Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah, Dr. Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, matan uku da aka gurfanar a gaban Kotun Majistare mai lamba biyar da ke Court Road sun haɗa da Hauwa Khamis, Sa’adatu Muhammad da Amani Ishaq.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ana zargin Amani Ishaq da yaɗa bidiyoyin rawa a shafinta na TikTok, waɗanda ake zargin sun ƙunshi abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.
Sai dai, bayanan da aka bayar ba su fayyace hukuncin da kotu ta yanke ko matakin da za a ɗauka na gaba ba.