Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaKano: Majalisa na shirin ladabtar da MB Aliyu kan zargin cin zarafin...

Kano: Majalisa na shirin ladabtar da MB Aliyu kan zargin cin zarafin Abba

Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin ɗaukar matakin ladabtarwa kan ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Nasarawa, MB Aliyu, bayan an shigar da ƙorafi a kansa kan zargin cin zarafin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Minjibir, A.A. Minjibir, ne ya gabatar da ƙorafin a gaban majalisar, inda ya danganta zargin da wani faifan bidiyo da ake zargin yana nuna MB Aliyu yana ɗaga kunnuwan zomo.

A yayin gabatar da ƙorafin, A.A. Minjibir ya bayyana cewa abin da ake zargin ɗan majalisar ya aikata ya saɓa wa ɗa’a da ƙa’idojin majalisar.

Shi ma ɗan majalisar Kumbotso, Hon. Muddassir Zawaciki, ya goyi bayan ƙorafin, inda ya ce a matsayinsa na bulaliyar majalisar, za su gana da MB Aliyu domin jin bayaninsa kan lamarin.

Ana sa ran majalisar za ta yanke shawarar matakin da ya dace bayan binciken lamarin da kuma la’akari da tanade-tanaden dokokinta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments