Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiICPC ta nemi kotu ta hana bayar da belin hadimin El-Rufai

ICPC ta nemi kotu ta hana bayar da belin hadimin El-Rufai

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta nuna adawa da buƙatar belin Jimi Lawal, wani hadimin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ake tuhuma a shari’ar zargin almundahana da kuɗi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa lauyan masu gabatar da ƙara, Ibrahim Mukhtar, ya bayyana cewa hukumar ta shigar da takardar adawa da buƙatar belin da aka gabatar a gaban kotu.

Sai dai lauyan bai bayyana dalilan da suka sa ICPC ta ƙi amincewa da bayar da belin ga Jimi Lawal ba.

Matakin na ICPC na zuwa ne yayin da shari’ar zargin almundahana da kuɗin ke ci gaba da gudana a kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments