Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta gargaɗi jama’a kan wani sanarwa na bogi da ake yaɗawa a intanet dangane da ’yan takarar gwamna a jihohi shida.
Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Zamfara, Gombe, Delta, Filato, Yobe da Kano. Hukumar ta ce sanarwar ba daga gare ta ta fito ba, kuma babu wani sanarwa na musamman da ta fitar kan ’yan takarar gwamna a jihohin.
INEC ta buƙaci jama’a su yi watsi da sanarwar tare da guje wa sake yaɗa ta, domin kada ta ruɗi al’umma.
Hukumar ta kuma shawarci ’yan Najeriya su riƙa tabbatar da sahihancin bayanan zaɓe ta shafukanta na hukuma, da suka haɗa da inecnigeria.org da shafukan ta na sada zumunta da aka tantance.
INEC ta jaddada cewa za ta ci gaba da samar da sahihan bayanai kan zaɓe, tana mai kira ga jama’a da su dogara da ingantattun hanyoyin samun labarai domin guje wa yaɗa bayanan ƙarya.