Gwamnatin Tarayya ta bayyana adawarta ga kudirin Majalisar Dattawa na yin gyara ga dokar yaki da ta’addanci domin kakaba hukuncin kisa, ba tare da zabin tara ba, kan dukkan laifukan garkuwa da mutane.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, ya bayyana matsayar gwamnatin a wani taron jin ra’ayoyin jama’a da Majalisar Dattawa ta shirya, inda ya gargadi cewa irin wannan doka na iya haifar da matsaloli ga hadin gwiwar Najeriya da kasashen duniya wajen yaki da ta’addanci.
Fagbemi ya ce kasashe da dama ba sa amincewa da mika wadanda ake zargi idan za a yanke musu hukuncin kisa, lamarin da ka iya sa ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane su samu mafaka a kasashen waje.
Ya kara da cewa kotunan kasashen waje suna mika wadanda ake nema bisa dalilan kare hakkin dan Adam idan hukuncin kisa na cikin dokar da za a yi amfani da ita.
An bayyana hakan ne a yayin taron jin ra’ayoyi kan kudirin gyara dokar hana yaki da ta’addanci, tare da tattaunawa kan soke da sake gabatar da dokar.