Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin buɗe ilahirin makarantun Unity 47 mallakinta da ke sassan jihohin ƙasar, waɗanda ta rufe a farkon watan nan sakamakon matsalolin tsaro da suka ta’azzara suke kuma barazana ga ɗaliban da ke makarantu.
Ma’aikatar Ilimi ta Najeriyar ce ta bayyana shirin buɗe makarantun a cikin wata rubutacciyar sanarwa da ta raba wa manema labarai.
Tun farko mahukuntan Najeriyar sun kulle makarantun ne sakamakon ta’azzarar sace-sace ɗalibai da ƴan bindiga suka faro a watan jiya, wanda ya kai ga sace ɗaliba 24 na sakandiren ‘yan mata a jihar Kebbi da kuma wasu fiye da 200 daga wata Sakandiren Katolika da ke Neja.
Duk da gargaɗin masanan tsaro dama tsokacin da wasu fitattu a ɓangaren na Ilimi suka yi game da illar da matakin kulle makarantun ka iya haifarwa, gwamnatin Najeriyar ta yi gaban kanta wajen kulle makarantun.