Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKada INEC ta kuskura ta fifita APC a zaben 2027 – ADC...

Kada INEC ta kuskura ta fifita APC a zaben 2027 – ADC PCC

ADC PCC ya nemi INEC ta ci gashin kanta ba wai bin umarnin APC ba

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ADC-PCC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta zama mai gaskiya a shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Kwamitin ya kuma buƙaci hukumar ta mayar da hankali kan karɓar katunan zaɓe na PVC, tana mai cewa yawan mutanen da suka yi rajistar zaɓe ba shi da amfani sosai idan waɗanda suka cancanta ba su samu katunansu ba.

ADC-PCC ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Laraba, bayan taron manema labarai na INEC da aka gudanar ranar Talata.

Kwamitin ya ce ɗan takararta na shugaban ƙasa a shirye yake ya shiga zaɓen 2027, matuƙar INEC ta tabbatar da zaɓen da zai kasance cikin ’yanci, adalci, gaskiya, tare da kare shi daga tashin hankali da magudi.

Ologbondiyan ya ce dole INEC ta nuna ’yancinta ta hanyar ƙin amincewa da duk wani yunƙurin jam’iyyar APC na yin tasiri kan shawarwarinta ko ayyukanta.

Ya ce wallafa alkaluman masu rajistar zaɓe ba zai isa ba idan waɗanda suka yi rajistar ba su samu katunan PVC ba.

“Karanta alkaluman rajista ba komai ba ne. Abin da ya fi muhimmanci shi ne adadin katunan da ’yan Najeriya suka karɓa a zahiri. Abin da ke bai wa ɗan ƙasa damar yin zaɓe a ranar zaɓe ba wai sunansa yana cikin wata rajista ba ne, illa katin PVC yana hannunsa.”

ADC-PCC ta nuna damuwa kan zargin samun tsaiko na ofis da jinkiri a wuraren karɓar PVC, musamman a wuraren da ta bayyana a matsayin sansanonin jam’iyyun adawa.

“Mun buƙaci INEC ta kasance mai zaman kanta kuma kada ta karɓi umarni daga APC. Dole INEC ta kasance mai adalci, ba ta yi aiki kamar wani ɓangare na jam’iyyar da ke mulki ba,” in ji Ologbondiyan.

Ya ce ADC za ta nemi a tabbatar da cikakken bin Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe a dukkan matakan gudanar da zaɓen.

“ADC ba za ta yarda da wani abu da bai kai ga bin dokokin zaɓenmu ba. Muna buƙatar cikakken gaskiya da bin ka’idojin da suka dace tun daga rajista har zuwa sanar da sakamakon zaɓe.”

Kwamitin ya kuma ce yana sa ido kan ayyukan INEC gabanin zaɓen, yana mai cewa ’yan Najeriya da kuma ƙasashen duniya su ma suna kallon yadda tsarin ke gudana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments