Ƙungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya (NUP) reshen Jihar Kaduna ta bayyana goyon bayanta ga Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, domin ya sake tsayawa takarar gwamna a karo na biyu.
Ƙungiyar ta bayyana Uba Sani a matsayin “gwamnan da ke tausaya wa ’yan fansho” a yayin wata ziyarar girmamawa da ta kai masa a gidan gwamnati da ke Kaduna ranar Talata.
Sakataren NUP na jihar, Alhassan Musa, ya ce gwamnatin Sanata Uba Sani ta fitar da sama da Naira biliyan 21 domin biyan bashin alawus-alawus na ritaya da tallafin rasuwa cikin shekaru uku.
Musa ya ce wannan adadi ba a taɓa samun irinsa a tarihin jihar ba, yana mai cewa gwamnatin da ta gabata ta biya sama da Naira biliyan 37 cikin shekaru takwas.
Ya ce a yanzu ’yan fansho na karɓar haƙƙoƙinsu a kan lokaci, sabanin a baya, lokacin da wasu ’yan fansho na ƙananan hukumomi ke samun kuɗinsu makonni biyu zuwa uku bayan lokacin da ya kamata.
“Cikin shekaru uku na mulkinka, ka samu damar biyan sama da Naira biliyan 21, wanda a tarihin Jihar Kaduna ba a taɓa samun irin wannan ba,” in ji shi.
“Wani lokaci ma, ’yan fansho na samun haƙƙoƙinsu kafin ma ma’aikatan gwamnati su karɓi albashinsu. Wannan ci gaba ne mai kyau wanda muke matuƙar yaba maka a kansa.
“Muna tabbatar maka cewa za mu ci gaba da mara wa gwamnatinka baya. Haka kuma za mu goyi bayan ƙoƙarinka na neman wa’adi na biyu. Mun zo ne domin mu sanar da kai cewa ’yan fanshon Jihar Kaduna suna bayanka da kashi 100 cikin 100, ranka ya daɗe.”
Mataimakin shugaban ƙasa na NUP, Abdullahi Onuh, ya ce ƙungiyar tana da kusan ’yan fansho 16,000 a Jihar Kaduna.
Da yake mayar da martani, gwamnan ya ce gwamnatinsa tana mutunta tare da daraja tsofaffi, yana mai cewa a ƙarshe kowane ma’aikaci zai yi ritaya.
Uba Sani ya ce biyan ’yan fansho haƙƙoƙinsu yadda ya kamata zai ƙarfafa gwiwar ma’aikatan da ke kan aiki.
Ya ce an ɗauki gwamnatinsa a matsayin mai tausaya wa ’yan fansho ne saboda irin dogon yaƙin da ya yi wajen kare muradun ma’aikata da sauran masu rauni a cikin al’umma.