Ma’aikatar Harkokin Wajen Kuwait ta yi Allah wadai da harin da kungiyar Houthi ta kai kan wata tashar wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga Masallacin Annabi S.A.W da ke Madina.
Ma’aikatar ta bayyana harin a matsayin abin da ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa, tare da bayyana cewa kai hari kan kadarorin fararen hula ba abin amincewa ba ne.
Kuwait ta ce harin na iya ƙara haifar da tashin hankali da tsokana, tare da ɓata ran Musulmi a sassa daban-daban na duniya, musamman ganin cewa wuraren ibada masu tsarki ne.
Ma’aikatar ta kuma jaddada cikakken goyon bayanta ga Masarautar Saudi Arabia, tare da cewa tana goyon bayan duk matakan da ƙasar za ta ɗauka domin kare ikonta, tsaronta da lafiyar al’ummarta.
Kuwait ta ƙara jaddada cewa tsaron Saudi Arabia na da alaƙa da tsaron Kuwait da sauran ƙasashen mambobin Majalisar Haɗin Kan Kasashen Larabawa na Tekun Fasha (GCC).