Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabarai“Kuri’a ita ce zaɓe, ’yan Arewa sun fi ’yan Kudu yawa kuma...

“Kuri’a ita ce zaɓe, ’yan Arewa sun fi ’yan Kudu yawa kuma sun fi yawan ƙuri’a” – Tanko Yakasai

Yayin da Najeriya ke bikin cikar shekaru 66 da samun ’yancin kai, tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Tanko Yakasai, ya yi magana kan muhimmancin ƙuri’a da kuma tasirin yawan masu kaɗa ƙuri’a a zaɓukan ƙasar.

Yakasai ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Iconic Times, inda ya ce ƙuri’a ita ce ginshiƙin zaɓe, yana mai cewa Arewacin Najeriya na da yawan jama’a da kuma masu kaɗa ƙuri’a.

A cewarsa, yawan ƙuri’un da ake samu daga yankuna na taka muhimmiyar rawa wajen zaɓe, musamman a lokacin da ‘yan siyasa ke neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a.

Yakasai ya ce: “Kai ya waye, ƙuri’a ita ce zaɓe. Mutanen Arewa sun fi Kudu yawa, kuma idan zaɓe ya zo, sun fi yawan ƙuri’a.”

Ya bayyana wannan ne yayin da ake bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai daga mulkin Birtaniya, tare da ƙara tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Yakasai ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su fahimci muhimmancin ƙuri’arsu tare da amfani da damar zaɓe wajen bayyana ra’ayinsu kan shugabannin da suke son su wakilce su.

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa ya ce yawan masu kaɗa ƙuri’a da yadda suke amfani da haƙƙinsu na zaɓe na daga cikin muhimman abubuwan da ke bayyana ra’ayin jama’a a tsarin dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments