Ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan jama’a da tallafa wa ’yan Yarbawa da ke zaune a Jihar Kano, da nufin samun goyon bayan mutane miliyan ɗaya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Abejide, wanda ke wakiltar mazabar Yagba ta tarayya a Jihar Kogi, ya bayyana shirin ne bayan ƙaddamar da kwamiti mai mambobi 27 da zai jagoranci ayyukan a ƙananan hukumomi 44 na Kano.
Ya ce shirin zai mayar da hankali kan zawarawa, matasa, mata, ’yan sana’a, ’yan kasuwa da sauran masu buƙatar tallafin tattalin arziki.
Da yake jawabi a fadar Oban Yarbawa na Kano, Abejide ya ce shirin zai haɗa tallafin tattalin arziki da wayar da kan al’umma gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya kuma umarci kwamitin da ya tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon tallafin, musamman ga mutanen da suke cikin buƙata.
Mai kula da kwamitin, Seyi Olorunsola, ya ce za su fifita muradun al’umma tare da yin aiki da masu ruwa da tsaki domin gano waɗanda suka cancanci amfana da shirin.