Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce shirin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur na iya sa farashin litar fetur ya koma tsakanin Naira 400 zuwa Naira 500.
Melaye ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce manufar ADC ita ce samar da yanayin da zai rage tsadar rayuwa ga ’yan Najeriya.
A cewarsa, rage farashin fetur zai iya taimakawa wajen rage kuɗin sufuri, wanda hakan zai iya shafar farashin kayayyaki da sauran harkokin tattalin arziki.
Atiku Abubakar ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027. Sai dai gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta soki wannan shiri, tana mai cewa zai iya yin illa ga tattalin arzikin ƙasa.
Shi ma Peter Obi ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi, amma ya ce zai fara da yaƙi da cin hanci da rashawa kafin ɗaukar wannan matakin.