Sunday, October 18, 2026
HomeTsaro'Yan bindiga sun hallaka sakataren lafiya a Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun hallaka sakataren lafiya a Jihar Katsina

Marigayin, Sa’adu Dantutture, ya taba rike mukamin daraktan kula da lafiya a matakin farko a Funtua

An kashe Sakataren Lafiya na Karamar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, Sa’adu Dantutture, bayan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a garinsu na Dantutture da ke Karamar Hukumar Kafur.

Dantutture, wanda ya taba zama Daraktan Kula da Lafiyar Matakin Farko a Karamar Hukumar Funtua, na komawa gida ne bayan an kai hari garin a daren Laraba, inda ’yan bindigar suka sace shi.

Wani mazaunin garin, Kabir Ado Mai Unguwa, ya ce maharan sun shiga garin da misalin karfe 11 na dare, inda suka wawure wasu shaguna tare da yin awon gaba da Dantutture.

Ya ce daga bisani ’yan bindigar sun kashe shi a lokacin da suke kokarin barin garin.

“Da farko sun yi garkuwa da shi, suka tafi da shi bayan sun wawure wasu daga cikin shagunanmu. Amma yayin da suke barin kauyen, sai suka kashe shi,” in ji shi.

Mai Unguwa ya kara da cewa dakarun rundunar sojin Najeriya ta Brigade 17, tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai, sun yi arangama da maharan.

Rahotanni sun ce an kashe wasu mutane uku da ake zargin ’yan bindiga ne, yayin da wani ya tsere bayan ya bar makaminsa a wurin.

An yi jana’izar Dantutture a garinsu, inda iyalansa, abokan aikinsa, abokansa da mazauna yankin suka halarta cikin alhini da addu’o’i.

Matar marigayin, Fatima Sa’adu, ta bayyana mijinta a matsayin mutum mai saukin kai kuma mai kishin hidimar al’umma.

“Marigayi mijina mutum ne mai son jama’a. Ya rayu cikin sauki da tawali’u sosai. Wannan iyali ya shiga wani babban bala’i sakamakon rasuwarsa,” in ji ta.

Ta roki gwamnati da ta kara kaimi wajen yaki da rashin tsaro tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kafin rasuwarsa, Dantutture ya yi aiki a matsayin Daraktan Kula da Lafiyar Matakin Farko a Karamar Hukumar Funtua, kafin daga bisani ya zama Sakataren Lafiya na Malumfashi.

Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Abdulmutallib Sulaiman Goya, wanda ya kai ziyara ga iyalan marigayin, ya bayyana shi a matsayin ma’aikacin gwamnati mai gaskiya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa bil’adama hidima.

Dan marigayin, Mu’azzam Sa’adu, ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakan dakile ayyukan ’yan bindiga.

“Muna son zaman lafiya. Mun cancanci a kare mu. Babu wani iyali da ya kamata ya fuskanci irin abin da muke ciki a yau,” in ji shi.

Wani abokin marigayin, Alhaji Rabi’u Dantutture, ya bayyana kisan a matsayin babban rashi mai radadi.

“Mutum ne mai kirki da tawali’u sosai, kuma mutum ne da ya sadaukar da kansa ga duk abin da ya zaba ya yi. Ban taba tunanin cewa wata rana zan tsaya a nan ina zaman makokin mutuwarsa ba,” in ji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce zai binciki rahoton kafin ya mayar da martani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ba ta sake bayar da wani bayani kan lamarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments