Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gudanar da atisayen motsa jiki da wasanni, tare da sake horas da jami’anta kan fareti da ladabtarwa, domin ƙara ƙwarewa da inganta ayyukan tsaro.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar 23 ga Satumba, 2026, ta ce an gudanar da atisayen motsa jikin ne a ranar Laraba a filin ƙwallon ƙafa na hedikwatar rundunar da ke Barikin ’Yan Sanda na Bompai, Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa atisayen ya ƙunshi motsa jiki, tsere, wasan ƙwallon ƙafa da sauran ayyukan da ke taimakawa wajen ƙarfafa jiki da juriya.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, wanda mataimakinsa mai kula da ayyukan rundunar, DCP Lawal Isa Mani, ya wakilta, ya jaddada muhimmancin lafiyar jiki da ta kwakwalwa wajen gudanar da aikin ’yan sanda yadda ya kamata.
Ya ce jami’in da ke cikin ƙoshin lafiya zai fi kasancewa cikin shirin tunkarar ƙalubalen tsaro, tare da bayyana cewa motsa jiki na taimakawa wajen rage damuwa, ƙara kaifin lura da inganta lafiyar kwakwalwa.
Ya kuma buƙaci jami’an su riƙa motsa jiki akai-akai tare da zuwa gwajin lafiya lokaci-lokaci.
A wani ɓangare kuma, rundunar ta gudanar da atisayen sake horas da jami’anta kan fareti a ranar Talata, 22 ga Satumba, a filin fareti na hedikwatarta da ke Bompai.
An ce an shirya atisayen ne domin ƙarfafa ladabi, bin umarni, sarrafa jami’ai da kuma kyakkyawar ɗabi’ar aiki.
Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa fareti ginshiƙi ne na ladabtarwa da ƙwarewar jami’an ’yan sanda, yana mai cewa za a ci gaba da horas da jami’ai domin su kasance cikin shiri da kuma iya tunkarar ƙalubalen tsaro na zamani.
Rundunar ta tabbatar wa al’ummar Kano cewa za ta ci gaba da mayar da hankali kan horaswa, walwala da jin daɗin jami’anta domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ta kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.