Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da kwamitin mutum 10 domin binciken mutuwar masu haƙar ma’adanai 37 da ke tsare a hannun hukumar NSCDC a jihar Neja.
Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ƙaddamar da kwamitin a Abuja, bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Jonathan Kure, yayin da Farfesa Isa Hayatu Chiroma zai kasance sakataren kwamitin. Sauran mambobin sun haɗa da AIG Hosea Hassan Karma mai ritaya, Farfesa Olayinka Buhari da lauya Deji Adeyanju.
Haka kuma akwai wakilan masarautar Minna da gwamnatin jihar Neja, da kuma Alhaji Liman Sulaiman na ƙungiyar masu haƙar ma’adanai ta ƙasa.
Masu haƙar ma’adanan 37 sun rasu ne yayin da suke tsare a hannun NSCDC. Zuwa yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwarsu ba, yayin da binciken kwamitin zai mayar da hankali wajen gano abin da ya faru.