Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta yi watsi da zargin da wasu ’yan siyasar adawa ke yi na cewa gwamnati na amfani da hukumar EFCC wajen cin zarafin masu adawa da gwamnati.
Fadar ta kuma musanta zargin cewa dimokuraɗiyya na cikin barazana saboda wasu manyan ’yan siyasa suna sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 14 ga Disamba, ya bayyana cewa waɗannan zarge-zargen yunƙuri ne na rikitar da al’umma domin neman riba ta siyasa.
Sanarwar ta ce wasu ’yan siyasar adawa na yin surutu ne kawai saboda gazawarsu a siyasa.
Sanarwar ta ce: “zargin da ake yi kan yadda manyan ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ba ya da tushe, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ’yan ƙasa ’yancin shiga kowace jam’iyya da suke so ko sauya ra’ayi a duk lokacin da suka ga dama.”
“Babu wanda aka tilasta masa shiga APC, kuma masu sauya sheƙar suna yin hakan ne saboda abin da suka gani a matsayin nasarorin shirye-shiryen gyaran tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu.” in ji sanarwar.
Game da zargin cewa “Gwamnati na amfani da hukumar EFCC a matsayin makami, Fadar Shugaban Kasa ta jaddada cewa hukumar na da ’yancin cin gashin kanta bisa doka, kuma tana gudanar da aikinta ba tare da tsoma bakin kowa ba.
Sanarwar ta ce aikin EFCC shi ne bincike da gurfanar da masu aikata laifukan kuɗi ba tare da la’akari da jam’iyya ko matsayin mutum ba, tare da ƙara da cewa Shugaba Tinubu ba ya ba da umarni kan wanda za a bincika ko a gurfanar.
Fadar shugaban ƙasa ta kuma yi kira ga ’yan siyasar da ake bincike da su tsaya su kare kansu a gaban doka idan sun san ba su da laifi, maimakon yin zarge-zargen siyasa.