Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, ya ce ya kamata ’yan Najeriya su amince da cewa suna da wani kaso na alhaki kan matsalar rashin ingantaccen shugabanci da suke yawan korafi a kai.
Ndume ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da littafin Military Transformational Leadership in Action: The Buratai Era, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro da Suites ta Rundunar Sojin Najeriya da ke Asokoro, Abuja.
Sanatan ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake mayar da martani ga kalaman Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda ya yi suka kan yadda ’yan siyasa ke amfani da ƙabilanci da addini wajen neman goyon bayan jama’a, da kuma yadda hakan ke shafar tsaro da shugabancin ƙasa.
A cewar Ndume, bai kamata a ɗora dukkan alhakin matsalolin shugabanci kan ’yan siyasa kawai ba, domin ’yan siyasa daga cikin al’umma suke fitowa, kuma su ne ’yan ƙasa ke zaɓe.
Ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su taka muhimmiyar rawa wajen gyara tsarin zaɓe, musamman ta hanyar yaƙi da magudin zaɓe da kuma yin la’akari da cancanta da halayen ’yan takara kafin su ba su goyon baya.
Ndume ya ƙara da cewa ingancin shugabanci yana da alaƙa da irin zaɓin da jama’a suke yi, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su ƙara shiga cikin harkokin siyasa da dimokuraɗiyya domin su taimaka wajen samar da irin shugabancin da suke muradi.