Wasu malaman addinin Musulunci mata daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce malaman matan sun yanke wannan shawara ne bisa ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewarsa, goyon bayan da malaman matan suka bayar ba wai saboda wata manufa ta kashin kai ba ce, illa saboda irin nasarorin da suka ce gwamnatin Tinubu ta samu musamman a fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, noma da ayyukan more rayuwa.
Uba Sani ya ƙara da cewa malaman matan sun yaba da yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin bai wa yankuna daban-daban damar cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati ba tare da nuna bambanci ba.
Ya kuma ambaci shirye-shiryen Asusun Ba da Lamunin Ilimi ga Ɗaliban Najeriya, wato NELFUND, da kuma shirye-shiryen koyar da sana’o’i da fasahohi na TVET, yana mai cewa yankin Arewa ya amfana sosai da waɗannan shirye-shirye.
Gwamnan ya ce goyon bayan malaman matan ya nuna yadda wasu sassa na al’ummar Arewa ke kallon ayyuka da manufofin gwamnatin Tinubu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.