Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeSaudiyya ta rufe babban bututun man kasar bayan hare-haren Iraq

Saudiyya ta rufe babban bututun man kasar bayan hare-haren Iraq

Saudiyya ta rufe wani muhimmin bututun jigilar mai na East-West mai tsawon kilomita 1,200, bayan wani hari da jirage marasa matuƙa da aka harba daga Iraq suka kai.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake fargabar hare-haren na iya shafar muhimman hanyoyin samar da makamashi da kuma jigilar kayayyaki.

An rufe bututun East-West ne a ranar Juma’a, 11 ga watan Satumban 2026, a matsayin matakin kariya bayan harin.

Bututun yana da matuƙar muhimmanci ga Saudiyya saboda yana ba ta damar jigilar mai ba tare da dogaro da mashigar Hormuz ba.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta tabbatar da cewa harin ya jikkata wasu mutane tare da haddasa lalacewar wasu kadarori.

Sai dai hukumomin ƙasar sun ce ana ci gaba da bincike domin gano cikakken girman barnar da harin ya haifar.

A nata ɓangaren, gwamnatin Iraq ta tabbatar da cewa jiragen marasa matuƙan da suka kai harin sun taso ne daga jihar Maysan da ke kusa da iyakar Iran.

Hukumomin ƙasar sun ce an fara bincike kan lamarin, yayin da aka cire wani babban kwamandan soja daga mukaminsa.

Saudiyya ta ce ba za ta gaggauta kai harin ramuwar gayya ba, bayan kiran da Firaministan Iraq ya yi.

A cewar gwamnatin Saudiyya, za ta mara wa gwamnatin Iraq baya wajen ɗaukar matakan da za su hana ƙasar zama wajen da ake ƙaddamar da hare-hare kan maƙwabtanta.

Rahotanni sun nuna cewa bututun East-West yana jigilar wani kaso mai yawa na man da ake samarwa a duniya.

Rufe shi na iya ƙara matsin lamba kan kasuwar ɗanyen mai da kuma hanyoyin samar da makamashi, musamman a wannan lokaci da rikici ke ƙara ƙamari a yankin.

Harin ya kuma zo ne yayin da mayakan Houthi da Iran ke mara wa baya ke ci gaba da ƙara ƙarfi a Yemen.

Kungiyar Houthi ta yi ikirarin mallakar mashigar Bab al-Mandab, wata muhimmiyar hanyar ruwa da ke haɗa Bahar Maliya da hanyoyin zuwa mashigar Suez.

Sai dai mayakan Houthi sun bayyana cewa zirga-zirgar jiragen ruwa za ta kasance lafiya ga sauran ƙasashe da kamfanoni, ban da jiragen ruwan Saudiyya.

A wani bangaren kuma, an ruwaito cewa Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya tuntubi Shugaban Amurka, Donald Trump, kan halin da ake ciki, inda aka ce ya nemi a ƙara ɗaukar matakai kan mayakan Houthi da ke Yemen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments