Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeZan ba duk wani baligi a Amurka kyautar $5,000 idan Republican ta...

Zan ba duk wani baligi a Amurka kyautar $5,000 idan Republican ta lashe zaben Nuwamba – Trump

Ya ce sharadin kawai shi ne a kashe kuɗin a cikin Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce zai bai wa kowane baligi ɗan ƙasar Dala 5,000 idan jam’iyyarsa ta Republican ta samu rinjaye a majalisun dokokin ƙasar biyu a zaɓen da za a gudanar a watan Nuwamba.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani kan yadda za a samar da kuɗin ko kuma ko shirin bai saba wa doka ba.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron farko na jam’iyyar Republican da aka shirya domin tunkarar zaɓen tsakiyar wa’adi. Ya yi amfani da taron wajen ƙarfafa magoya bayansa gabanin zaɓen da ake ganin yana da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyar.

Trump ya ce sharadi guda da yake da shi shi ne dole ne a kashe kuɗin a Amurka.

Duk da raguwar amincewar jama’a da shugabancinsa da aka samu a wasu ƙuri’un jin ra’ayi, Trump ya buƙaci mahalarta taron da su fito ƙwarai su kaɗa ƙuri’a.

Ya kuma ce su yi hakan kamar shi kansa ne ke takarar zaɓen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments