Iyalan mamacin sun bayyana cewa mutumin na kan babur ne lokacin da ƴan sanda suka fara binsa, lamarin da ya sanya shi ƙara gudu a babur ɗin har ta kai ga ya yi haɗari.
Duk da cewa iyalin mamacin sun amince cewa ɗan uwansu na tuƙa babur ɗin ba tare da lasisi ba, amma sun yi amannar cewa ƴan sandan na iya amfani da cikakkiyar ƙwarewa wajen tunkarar ɗan uwansu, ba wai cikin tashin hankali har ta kai shi ga rasa ransa ba.
Wannan lamari dai ya haddasa fargabar yaɗuwar zanga-zanga, ganin yadda jama’a suka fusata game da jami’an tsaro.
Lamarin na faruwa ne a yayin da Tunisia ke shirin bikin tunawa da juyin juya halin watan Janairu na shekarar 2011, da ya jawo gagarumin sauyi a ƙasashen Larabawa.
A baya-bayan, ana samun ƙaruwar zanga-zanga da kuma kira daga babbar ƙungiyar ƙwadago ta UGTT na shiga yajin aikin ƙasa baki ɗaya a watan gobe.
A halin da ake ciki, dubban mutane sun shafe makonni suna zanga-zanga a birnin Gabes na Kudancin ƙasar, suna buƙatar a rufe wani kamfanin sinadarai bisa dalilan kare muhalli da lafiyar jama’a.
Shaidu sun ce masu zanga-zangar a Kairouan sun riƙa jifa da duwatsu, kwalaben man fetur masu wuta, da fitilu masu walƙiya, tare da toshe hanyoyi ta hanyar ƙona tayoyi, abin da ya sa ƴan sanda suka tarwatsa taron da hayaƙi mai sa hawaye.
Iyalan mamacin sun ce bayan ƴan sanda sun kama shi, an riƙa dukansa bayan ranukan da ya samu daga haɗarin da ya yi, duk da cewa mutumin ya tsere daga hannun jami’an tsaro bayan kai shi asibiti, amma ya mutu ranar Juma’a sakamakon raunin da ya samu a ka.
Gwamnati ba ta yi martani game da lamarin ba, yayin da ƴan uwan mamacin suka ce ba za su yi shiru ba, kuma za su tayar da gagarumar zanga-zanga idan ba a hukunta waɗanda ke da alhakin asarar ran ɗan uwansu ba.