Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taya Mataimakin Shugaban Tarayyar Najeriya, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana Shettima a matsayin gogaggen ɗan siyasa, ƙwararren mai gudanar da mulki kuma shugaba mai hangen nesa, wanda ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban Najeriya.
Gwamnan ya yaba da jarumtakar mataimakin shugaban kasar, tawali’unsa da jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima. Ya ce kwarewar Shettima a harkokin mulki ta kasance babbar gudunmawa ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar gwamnan, shekarun Shettima a hidimar gwamnati, musamman lokacin da yake gwamnan Jihar Borno, sanata da kuma yanzu a matsayin mataimakin shugaban kasa, sun nuna yadda ya himmatu wajen inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Gwamnan ya kuma yaba da basirar Shettima, kishin kasa da kuma kokarinsa na karfafa hadin kan kasa da bunkasa tattalin arziki.
Gwamnan ya roki Allah Ya ba mataimakin shugaban kasar lafiya, hikima da karfin gwiwar ci gaba da yi wa kasa hidima.
Ya kuma yi masa fatan samun karin shekaru masu albarka da hidima mai amfani ga kasa.