Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeAmurka za ta janye sojoji 200 daga Najeriya

Amurka za ta janye sojoji 200 daga Najeriya

Amurka na shirin janye kusan sojoji 200 da ta kawo Najeriya domin taimakawa wajen yaki da kungiyoyi masu dauke da makamai, bayan da jami’an Amurka suka ce an samu gagarumar nasara a ayyukan yaki da ta’addanci.

Rahoton New York Times ya ce Pentagon na shirin kammala janyewar sojojin zuwa karshen watan Satumba. Sojojin sun taimaka wa Najeriya wajen musayar bayanan sirri, horas da jami’an tsaro da gudanar da wasu ayyukan yaki da ta’addanci.

Sai dai janyewar ba za ta kawo karshen hadin gwiwar soji tsakanin kasashen biyu ba, domin ana sa ran wasu kananan kungiyoyin masu horaswa da kwararrun bayanan sirri za su ci gaba da kasancewa a Najeriya.

Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan wani samame da aka gudanar a watan Mayu a yankin Tafkin Chadi, wanda ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, wanda Amurka ta bayyana a matsayin na biyu a jagorancin ISIS.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments