Birtaniya ta haramta wa wasu manyan kwamandojin kungiyar RSF ta Sudan shiga kasar, waɗanda ake zargi sun aikata munanan laifuka a birnin El-Fasher, tare da kwace kadarorinsu.
Mutanen dai sun haɗa da mataimakin shugaban RSF, Abdul Rahim Hamdan Dagalo, da wasu kwamandoji uku.
Laifukan da ake zargin su da aikatawa sun haɗa da kisan gwamman mutane, da kuma cin zarafi ta hanyar lalata.
Birtaniya ta ce shaidun da aka samu sun tabbatar da cewa ana barin mutane da yunwa, wasu kuma a yi musu fyade, wanda abu ne mai matuƙar tayar da hankali, kuma tana duba yiwuwar ƙaƙaba musu ƙarin takunkumai.
Birtaniya ta kuma ce za ta bayar da tallafin Dala miliyan 28 domin samar da kayan tallafi, sannan a kare mata da yara, wadanda lamarin ya fi shafa.