Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci Musulmi su yi koyi da kyawawan halaye da ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW), musamman tausayi, yafiya da zaman lafiya.
A cikin saƙonta na bikin Maulidi, wanda gidan talabijin na ARISE ya ruwaito, Remi Tinubu ta ce tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW) wata dama ce ga Musulmi su yi nazari kan rayuwarsa da kyawawan ɗabi’un da ya koyar.
Ta ƙara da cewa ya kamata bikin Maulidi ya kasance lokaci na tunatar da al’umma muhimmancin tausayi, haɗin kai, yafiya da zaman lafiya a tsakanin al’umma.