Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin janye tare da sake duba jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC na 2027.
An fitar da jerin sunayen ne a ranar Asabar, inda aka nada tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin.
Tinubu zai kasance shugaban kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, za su kasance mataimakan shugaban kwamitin.
Sai dai jerin sunayen ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar, musamman kan rashin sanya wasu manyan ’yan APC da suka taka muhimmiyar rawa a yakin neman zaɓen jam’iyyar a baya.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin ’yan jam’iyyar sun nuna damuwa kan tsarin rabon mukamai, wakilcin yankuna da kuma yadda aka tsara matsayin wasu manyan jami’an jam’iyyar da na gwamnati.
Daga cikin fitattun ’yan APC da ba su bayyana a jerin farko ba akwai tsohon Gwamnan Plateau, Simon Lalong; mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello; da wasu fitattun ’yan jam’iyyar da suka yi fice wajen yaƙin neman zaɓen APC a baya.
Bayan ce-ce-ku-ce da jerin ya haifar, Shugaba Tinubu ya umarci a janye jerin domin a sake duba shi tare da yin gyare-gyare da suka shafi tsarin kwamitin da wakilcin manyan ɓangarorin jam’iyyar.
Sai dai rahotannin da ake samu sun nuna cewa ba a bayyana cewa an sauya nadin Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta-Janar ba; abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne sake duba tsarin da kuma jerin mambobin kwamitin.
APC ta fitar da jerin kwamitin ne a yayin da jam’iyyar ke shirin fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027, bayan Tinubu ya samu tikitin jam’iyyar domin sake neman shugabancin Najeriya.