Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaGwamnan Kebbi ya sauya mataimakinsa a takarar 2027

Gwamnan Kebbi ya sauya mataimakinsa a takarar 2027

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zabi Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon abokin takararsa a zaɓen gwamna na 2027, inda ya maye gurbin mataimakinsa na yanzu, Sanata Umar Tafida.

Sakataren Tsare-tsare na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Suleiman Argungu, ne ya bayyana hakan a Birnin Kebbi ranar Lahadi.

Argungu ya ce an dauki matakin ne bisa shawarar ƙwararrun lauyoyi da suka yi nazari kan cancantar mataimakin gwamnan na yanzu.

Sai dai ya bayyana cewa Tafida ya amince da sauyin, yana mai cewa babu wata takaddama ko rashin jituwa tsakanin gwamnan da mataimakinsa.

Daga bisani, Argungu ya sanar da Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon abokin takarar Gwamna Nasir Idris a zaɓen 2027.

Ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da mambobin APC a jihar da su rungumi sauyin tare da haɗa kai domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments