Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benue ta gano wani jariri namiji da aka sace jim kaɗan bayan haihuwarsa a Asibitin Gboko da ke Ƙaramar Hukumar Gboko ta jihar.
An sace jaririn ne a safiyar Talata bayan wata mata da ta yi kama da ma’aikaciyar jinya ta ɗauke shi daga wajen mahaifiyarsa, bisa ikirarin cewa za ta kai shi domin ƙarin kulawa.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Benue, DSP Peter Aondongu, ya tabbatar da cewa an gano jaririn a ranar Alhamis tare da mayar da shi ga mahaifiyarsa a ofishin ’yan sanda na ‘A’ Division da ke Gboko.
Ya ce an kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin, inda wasu ke tsare a Gboko, yayin da aka kai wasu hedikwatar rundunar da ke Makurdi.
Sai dai kakakin ya ce ba a tabbatar da ainihin adadin waɗanda aka kama ba tukuna, yana mai cewa za a fitar da ƙarin bayani yayin da bincike ke ci gaba.
Mazauna Gboko sun ce an gano jaririn ne a daren Laraba bayan wani samame da ’yan sanda suka gudanar a yankin Adekaa, inda suka kama wani da ake zargi da safarar yara.
Sun ce an bi sawun wanda ake zargin ne ta hanyar bayanan sirri bayan ya yi tafiya daga Ƙaramar Hukumar Tarka zuwa yankin.