Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta amince da kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
NAHCON ta ce an amince da kamfanonin ne bayan an gudanar da cikakken bincike da tantancewa ta musamman, inda aka duba ƙa’idojin tsaron jiragen sama, ƙwarewar kamfanonin da kuma ƙarfin gudanar da ayyukansu.
Kamfanonin da aka amince da su sun haɗa da Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Aviation Services Limited.
Hukumar ta bayyana cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da cewa jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya ta kasance cikin tsari, aminci da inganci.