Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKwastam ta kama harsasai 3,300 da wasu kayayyakin da suka kai N365m

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da wasu kayayyakin da suka kai N365m

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), reshen iyakar Seme, ta kama harsasai 3,300 da ake zargin an yi ƙoƙarin shigo da su Najeriya ta kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), reshen iyakar Seme, ta kama harsasai 3,300 da ake zargin an yi ƙoƙarin shigo da su Najeriya ta kan iyaka ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamandan Kwastam na yankin Seme, Abdullahi Kaila, ya ce an kama harsasan ne cikin watanni biyu da suka gabata, tare da wasu haramtattun kayayyaki da jimillar ƙimarsu ta kai N365.1 miliyan.

Kaila ya ce kama harsasan na da matuƙar muhimmanci, saboda suna iya shiga hannun miyagu tare da taimakawa wajen aikata ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka.

Ya ce an miƙa harsasan da wanda ake zargin ya shigo da su ga sashen EOD na ’yan sandan Najeriya domin ajiya da ci gaba da bincike.

Daga cikin sauran kayayyakin da aka kama akwai buhunan tabar wiwi 373, kwalayen Tramaking 250mg guda 90, Royal Tapentadol 250mg guda 69 da sandunan sigari 310,000.

Hukumar ta kuma kama kwale-kwalen ruwa, babur ɗin ruwa, motar Toyota Land Cruiser 2017, Toyota RAV4 2016 da Nissan Versa 2010.

Kaila ya ƙara da cewa jami’an sun kuma kama wata mota da aka bayyana cewa tana ɗauke da kayan abinci, amma bayan bincike aka gano buhuna 1,306 na taliyar da wa’adin amfaninta ya ƙare, kowanne mai nauyin kilo 50.

Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ƙara ƙarfafa sa ido da tattara bayanan sirri domin dakile safarar makamai, ƙwayoyi da sauran haramtattun kayayyaki ta iyakokin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments