Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiASUU ta ba gwamnatin Gombe wa’adin kwanaki 14 ko kuma ta shiga...

ASUU ta ba gwamnatin Gombe wa’adin kwanaki 14 ko kuma ta shiga yajin aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Gombe (GSU), ta bai wa gwamnatin Jihar Gombe wa’adin kwanaki 14 da ta biya wasu hakkokin malamai, ko kuma ta fuskanci yajin aikin sai baba-ta-gani.

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Gombe (GSU), ta bai wa gwamnatin Jihar Gombe wa’adin kwanaki 14 da ta biya wasu hakkokin malamai, ko kuma ta fuskanci yajin aikin sai baba-ta-gani.

A wata sanarwa da shugabanta, Dr Mustapha S. Shehu, da sakatarensa, Dr Aliyu Usman Shelleng, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan rahoton kwamitin ziyarar Majalisar Zartarwar Ƙasa ta ASUU da ya duba matsalolin reshen.

ASUU ta ce idan gwamnati ba ta magance matsalolin ba cikin wa’adin, za a fara yajin aikin gaba ɗaya kuma ba tare da ƙayyadadden lokacin ƙarewa ba daga ranar Talata, 25 ga Agusta 2026.

Daga cikin buƙatun malaman akwai biyan bashin alawus ɗin Earned Academic Allowance na shekarun 2021 zuwa 2024, da kuma bashin tallafin albashi na kashi 25 da 35 cikin 100.

Haka kuma, malaman na neman aiwatar da mafi ƙarancin albashin N70,000 da biyan bashin mafi ƙarancin albashin N30,000.

Ƙungiyar ta kuma nemi cikakken aiwatar da yarjejeniyar 2025 tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU, da ƙarin alawus ɗin kula da ɗaliban digiri na biyu, koyarwa a aikace, horon masana’antu da tafiye-tafiyen karatu.

ASUU ta ce ta sha ƙoƙarin tattaunawa da gwamnatin jihar domin warware matsalolin, amma har yanzu ba a samu mafita ba.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa idan gwamnatin ba ta dauki mataki kafin cikar wa’adin, malaman za su fara yajin aikin da zai iya kawo tsaiko ga harkokin karatu a jami’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments