Mutum 15 sun mutu bayan motar bas da suke ciki ta kama da wuta sakamakon wani mummunan hatsarin mota a Jihar Neja, yayin da wasu 25 suka jikkata.
Kwamandar Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) a jihar, Aishatu Sa’adu, ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta ce motocin bas guda biyu ne suka yi taho-mu-gama a wata lanƙwasa da ke yankin Duma, a Karamar Hukumar Mokwa.
A cewarta, fasinjojin da ke cikin ɗaya daga cikin motocin sun ƙone ƙurmus bayan motar ta kama da wuta. Ta ƙara da cewa waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Bida da kuma Babban Asibitin Kutigi.
Sa’adu ta danganta hatsarin da gudun da ya wuce kima da wasu direbobi ke yi, tare da ƙoƙarin wuce motocin da ke gabansu ba bisa ƙa’ida ba. Ta ce waɗannan halaye na daga cikin abubuwan da ke haddasa munanan hatsuran ababen hawa.
Kwamandar FRSC ta gargadi direbobi da su riƙa bin ƙa’idojin hanya, musamman kiyaye gudun da ya dace da yanayin hanya, tare da guje wa wucewar ababen hawa ta hanyar da ka iya jefa rayukan fasinjoji cikin haɗari.