An samu motsawar ƙasa rauni a wasu sassan Babban Birnin Tarayya, Abuja, lamarin da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar ya faru a ranar Talata. Ministan Ma’adinai, Dele Alake, ya ce Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta gano motsin ƙasar ne ta ofishinta da ke Utako.
A cewar NGSA, an ji motsin ƙasar da misalin ƙarfe 11:23 na safe, inda aka bayyana cewa ya faru ne daga zurfin kilomita ɗaya a ƙarƙashin ƙasa kuma ya yi tafiyar kusan kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar. Hukumar ta ce ƙarfin motsin ya kai maki 1 zuwa 2 a ma’aunin Mercalli, wanda ba ya iya haddasa rushewar gine-gine ko barazana ga rayuka da dukiyoyi.
Bayan faruwar lamarin, Ministan ya umarci NGSA da ta ci gaba da gudanar da bincike tare da fitar da sabbin bayanai domin tantance halin da ake ciki da kuma yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati idan buƙatar hakan ta taso. Ya kuma tabbatar da cewa ana sa ido kan lamarin domin kare lafiyar jama’a.
Dele Alake ya buƙaci mazauna Abuja da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, yana mai jaddada cewa babu wata alamar haɗari daga motsin ƙasar da aka samu.
Ko da yake Najeriya ba ta cikin ƙasashen da girgizar ƙasa ke yawan faruwa, masana sun ce ana iya samun ƙananan motsin ƙasa a wasu lokuta musamman a Abuja da wasu jihohi, abin da ke nuna muhimmancin ci gaba da sa ido da kuma shirye-shiryen gaggawa idan buƙata ta taso.