Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMatasa na ta yawo da digiri babu aikin yi - Cardinal Onaiyekan

Matasa na ta yawo da digiri babu aikin yi – Cardinal Onaiyekan

Babban Faston ya ce rashin aikin yi ya hana matasa aure

Jagora a addinin Kirista a Najeriya, Cardinal John Onaiyekan ya bayyana cewa matsalar rashin aikin yi da ke ƙara ta’azzara a Najeriya ta kai ga hana matasa da dama masu digirin jami’a tunanin yin aure ko tsara makomarsu saboda rashin samun abin yi.

Tsohon babban Limamin Cocin Katolika na Abuja ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin tattalin arzikin ƙasar bayan ganawar da Kungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya ta yi da Shugaba Bola Tinubu.

Da yake hira a shirin Frontline na gidan rediyon Eagle 102.5 FM da ke Ilese-Ijebu a jihar Ogun, Onaiyekan ya ce ya kamata gwamnati ta rika auna nasararta da yadda rayuwar talakawan Najeriya take, ba wai da alkaluman tattalin arziki kamar GDP ko rahotannin Bankin Duniya ba

Onaiyekan ya bayyana rashin aikin yi a tsakanin matasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa dubban matasa da suka kammala jami’a na ci gaba da yawo da takardun digirinsu ba tare da samun aiki ba.

A cewarsa, wannan matsala ta hana matasa da dama tunanin yin aure, fara tara iyali da kuma tsara rayuwarsu ta gaba.

Ya ce:

“Abin takaici shi ne matasa da dama da suka sha wahalar kammala jami’a na yawo da digirinsu amma ba sa samun aiki. Saboda haka ba za su iya tunanin yin aure ba, balle kafa iyali ko tsara rayuwarsu. Wannan abin takaici ne ƙwarai.”

Cardinal ɗin ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba domin inganta rayuwar matasa marasa aikin yi, matsalar na iya haifar da mummunan sakamako ga ƙasar.

Ya kuma buƙaci gwamnati ta nuna ƙwazo wajen gudanar da mulki cikin gaskiya, adalci da kuma nuna daidaito ga kowa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments