Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiWatanni 6 kenan, masu garkuwa na ci gaba da riƙe mutane 176...

Watanni 6 kenan, masu garkuwa na ci gaba da riƙe mutane 176 a jihar Kwara

Bayan watanni shida, har yanzu mutane 176 da aka sace daga al'ummar Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane, lamarin da ya jefa iyalansu cikin matsanancin damuwa.

Bayan watanni shida, har yanzu mutane 176 da aka sace daga al’ummar Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane, lamarin da ya jefa iyalansu cikin matsanancin damuwa.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen yankin sun gudanar da zanga-zangar lumana domin neman gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Kwara da jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace. Sun bayyana cewa sama da kwanaki 170 sun shige ba tare da an samu nasarar kuɓutar da su ba.

Shugaban ƙauyen Woro, Umar Bio Salihu, wanda matarsa da ɗansa na cikin waɗanda aka sace, ya roƙi gwamnati da kada ta yi watsi da lamarin, yana mai cewa abin da suke buƙata shi ne a dawo da mutanensu cikin ƙoshin lafiya.

Shugaban Ƙungiyar Raya Kaiama, Mallam Yakubu Salihu, ya ce tsawaitar zaman mutanen a hannun masu garkuwa ya jefa iyalai da al’umma cikin tashin hankali, yana mai kira da a gaggauta ɗaukar matakin ceto su.

A nasa ɓangaren, jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin Kaiama, CSP Afiz Nafiu, ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa jami’an tsaro na ci gaba da aiki domin ceto waɗanda aka sace, tare da roƙon al’umma su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto mutanen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments