Lauya mai fafutukar kare haƙƙin al’umma, Abba Hikima Fagge, ya bayyana cewa a mahangar doka, kalaman da fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya yi kan Sheikh Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami na iya kai matsayin cin zarafi.
Fagge ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Fact, inda ya yi nuni da hukuncin Kotun Koli na shekarar 1978, wanda a cewarsa ya fayyace yadda doka ke kallon kalaman da za su iya tauye mutunci ko bata sunan mutum.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan sabuwar waƙar Dauda Kahutu Rarara, wadda ta jawo martani da muhawara a kafafen sada zumunta, musamman saboda yadda wasu ke ganin tana ɗauke da zambo ga ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Sheikh Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.