Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn haramtawa lauyoyi amfani da “Barista” a sunayensu

An haramtawa lauyoyi amfani da “Barista” a sunayensu

Alƙalin Alƙalai na Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta umarci dukkan lauyoyi, magatakardan kotu da sauran ma’aikatan sashen shari’a da su daina amfani da lakabin “Barista” a gaban sunayensu a duk wata mu’amala ta hukuma da Kotun Koli.

Umarnin na kunshe ne cikin wata takarda mai ɗauke da ranar 13 ga Yulin 2026, wadda Babban Magatakardan Kotun Koli, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu.

A cewar takardar, ci gaba da amfani da lakabin “Barista” bai dace da ƙa’idojin ƙwarewar aiki da Kotun Koli ke son tabbatarwa ba, saboda haka an umurci duk waɗanda abin ya shafa su daina amfani da shi a wasiƙu, takardun kotu, bayanan hukuma, katunan shaida da sauran mu’amaloli na hukuma.

Sabon umarnin ya fara aiki nan take, kuma ya shafi lauyoyi masu shari’a, magatakardan kotu, ma’aikatan sashen shari’a da duk wani lauya da ke hulɗa da Kotun Koli.

Haka kuma, an umurci shugabannin sassa da su tabbatar da cewa ma’aikatan da ke ƙarƙashinsu sun aiwatar da wannan umarni cikin gaggawa.

Kotun Koli ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin daidaita tsarin takardun hukuma da tabbatar da bin ƙa’idojin aiki iri ɗaya a fannin shari’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments