Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sabuwar gundumar Zarmakwai a Ƙaramar Hukumar Suru tare da ɗaga Mai Unguwar Tarasa zuwa matsayin hakimi a Ƙaramar Hukumar Birnin Kebbi.
A cewar gwamnatin jihar, an ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa tsarin shugabancin gargajiya, kusantar gwamnati da al’umma, da kuma inganta zaman lafiya da ci gaban yankuna.
Biyo bayan hakan, gwamnatin ta naɗa Alhaji Aliyu Abubakar Sarki a matsayin hakimin farko na Gundumar Zarmakwai, yayin da Alhaji Faruku Abubakar ya zama hakimin sabuwar Gundumar Tarasa.
Gwamnatin ta bayyana cewa an aiwatar da wannan sauyi ne bisa tanadin dokar Ƙananan Hukumomin Jihar Kebbi ta shekarar 2008, kuma matakin ya fara aiki nan take.
Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Garba Dutsinmari, ya buƙaci sababbin hakiman da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci, yana mai jaddada cewa cibiyoyin gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma.